Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yaye da BBC: Shirin bada magani kyauta

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mata da dama na mutuwa saboda rashin magunguna a lokacin haihuwa.

Wata kasida da ke kunshe da dabaru kan harkar kiwon lafiyar mata da kananan yara da Babban magatakardar majalisar dinkin duniya, Ban ki-moon ya jagoranta wacce aka kaddamar a bara ta bayyana ce wa a duk shekara kimanin yara miliyan takwas ne ke mutuwa kan dalilin da za'a iya kauce musu.

Haka kuma mata dubu dari 350 ke mutuwa sanadiyyar matsalolin kiwon lafiya da za'a iya magance su a lokacin da suke da juna biyu ko yayin haihuwa.

An dai kaddamar da kasidar ce a karshen babban taron da majalisar ta kira don duba nasarorin da aka samu wajen cimma muradun karni na majalisar dinkin duniya a shekaru goma da kuma zage dantsen da ake bukata don cimma muradun nan da shekarar 2015.

Kuma a tsokacin da banban magatakardar yayi yayin kaddamar da kasidar ya ce abu mafi mahimmanci wajen samar da ingantacen harkar kiwon lafiya ga mata da kananan yara tare da dorewar hakan na bukatar ingattacen tsarin kiwon lafiya da samun kwarrun ma'aita da ke tafiyar ta da tsarin. I

Ya kara da cewa akwai bukatar gwamnatoci da kungiyoyin kasa da kasa da masu zaman kansu, masu hannu da shuni da kwararru a fannin kiwon lafiya na da rawar da za su taka wajen ceton rayukan mata da kananan yara a fadin duniya.

Mr. Ban ya kuma ce zuba jari akan harkar kiwon lafiyar mata da yara zai yi matukar tasiri kan muradun karni na majalisar.

A lokacin kaddadamar da dabarun dai an bayyana cewa zuba jari a harkar kiwon lafiyar mata da yara ba wai kawai yin abinda ya dace a yi ba ne, ya na kaiwa ga samar da al'umma mi cike da kwanciyar hankali da kuma ci gaba.

Haka kuma magance matsalar karancin abinci mai gina jiki a tsakanin mata masu juna biyu da kananan yara na kaiwa ga karuwar kashi goma cikin dari na kudaden da mutum ke samu a fadin rayuwarsa.

Sannan majalisar ta yi nuni da cewa rashin tsaftar muhalli na iya janyo gudawa da wasu cututtuka da kan kai ga rage amfanin dan adam tare da hana yara zuwa makaranta.

To a Najeriya kamar a wasu kasashen dake nahiyar Afrika, wasu jihohin kasar sun bullo da shirin bada magani kyauta ko ma dauke nauyin harkar kiwon lafiya ga mata masu juna biyu da kananan yara 'yan kasa da shekaru biyar.

Sai dai wata babbar matsala da wasu ke kokawa da ita game da wannan ikirari na hukumomi shi ne shirin ya zama wani romon baka da ya saba fitowa daga bakin mahukunta. Shirin mu kenan na wannan makon. Ayi sauroro lafiya.