Sabuwar zanga-zangar ta barke a Syria

Masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Syria

Zanga -zangar nuna adawa da gwamnati ta sake barkewa a wurare daban daban a Syria inda rahotanni ke cewa dakarun kasar sun yi harbi kan tarin jama'a a garin Homs.

Wani da ya ga yadda al'amarin ya faru ya shaidawa BBC cewa mutane da dama sun ji rauni.

Dubban al'umma a sauran bangarorin kasar ciki harda garin Banias sun fito kan tituna domin yin zanga zanga.

Akwai rahotannin cewa shugaba Bashar Al Assad ya tura da dakarunsa domin su murkushe masu zanga zangar.

Da yake an hana 'yan jarida shiga kasar ta Syria don haka ba iya tabbatar da gaskiyar rahotannin ba.

Tun farko dai gwamnatin Syrian ta zargi shugaba Obama da haddasa tashin hankali a kasar, a cikin wani jawabin da ya yi a jiya Alhamis.