Majalisar dinkin Duniya ta nemi a tsagaita wuta a yankin Abyei

Garin Abyei
Image caption Garin Abyei

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran da a dakatar da bude wuta nan take a yankin Abyei na Sudan inda aka shafe rana ta uku a jere a tashin hankali.

A wata sanarwa da ta fitar, Majalisar Dinkin Duniyar ta ce tana nuna damuwa matuka da yadda ake amfani da makaman igwa tare da yin ruwan bam a yankin.

Tashin hankali na baya-bayanan ya barke ne a ranar Alhamis, lokacin da aka yiwa wani ayarin motocin soja na Arewacin Sudan kwanton bauna, abun da ya yi sanadiyar hallaka sojoji 22.

Dukan kabilun Dinka na kudancin kasar da Misseriya na Arewacin kasar, kowannensu na ikirarin cewa su suka mallaki yankin na Abyei, mai arzikin man fetur.

Wakilin BBC a Khartoum ya ce masu sharhi kan al'ammura na fargabar cewa wannan rikici zai iya jefa bangaren Arewaci da na Kudancin kasar ta Sudan cikin wani sabon yakin basasa.