Obama na shirya sake kaddamar da hari a Pakistan

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A wata ganawa da yayi da BBC, Shugaban kasar Amurka Barrack Obama ya ce a shirye yake da ya sake kaddamar da wani hari a Pakistan, domin farauto manya manyan shugabannin Kungiyoyin Al- Qaeda da Taliban.

Ya dai ce a yayinda Washington din ta kasance ta amince da 'yan cin Pakistan, ya zame masa tilas ya tabbatar da tsaron Amurka kuma.

Mammayar da Amurka ta kai a harabar gidan marigayi Osama bin Laden dai za'a ce itace ta wargaza yardar dake akwai a tsakanin Kasashen Amurka da Pakistan.

Sai dai duk da haka Barrack Obama na ganin cewa idan har kai harin daidai ne to a shirye yake da ya sake maimaita mataki makamancin wannan.

Ya dai ce a cikin aikinsu shine domin samar da tsaro ga Amurka, domin ba za su kyale wani ya ci gaba da shirya yanda zai kashe al'ummar Amurka ko al'ummar abokan su ba.

Inda ya sake cewa ba zasu bari wanann yunkurin ya haifar da wani abu ba tare da mun dauki mataki ba.

Sai dai a yayinda ya ce a shirye yake da ya kaddamar da hari ma akan shugaban kungiyar Taliban wato Mullar Omar, shugaban ya sauya harshe inda yake bayyana baki dayan fadan da su ke yi akan kungiyar Taliban a Afghanistan.

Ya dai ce tattaunawa da makiyan na Amurka zai kasance cikin siyasar su, sai dai ba'a kai ga fara wannan tattaunawar ba.