An rantsar da Alassane Ouattara a matsayin shugaban kasa

Alassane Ouattara Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Alassane Ouattara

Watanni shidda bayan zaben shugaban kasar Cote-D'Ivoire, wanda aka yi ta takaddama a kai, an yi bikin rantsar da Mr Alassane Ouatarra a matsayin zababben shugaban kasar.

Daga cikin masu halartar wannan rantsarwa har da shugaban Faransa Nicholas Sarkozy.

Kimanin mutane dubu uku ne suka rasa rayukansu sakamakon rikicin da ya biyo bayan wannan zabe.