Fada tsakanin dakaru da mayakan sa kan Pakistan

Jami'an tsaro a Pakistan sun yi ta bata- kashi tsakaninsu da wadansu mayakan sa kai da suka kai musu farmaki a sansanin soji dake garin Karachi a cikin dare.

Mayakan dauke da makamai sun dannan cikin sansanin ne in da suka tada wasu abubuwa dake haddasa wuta tare kuma da lalata wasu jiragen sama.

Rahotanni dai na cewa kimanin mutane goma sha daya ne suka rasu, sannan kuma an yi garkuwa da mutane da dama, ciki har da ma'aikatan sojin 'yan kasar Sin.

Kungiyar Taliban reshen Pakistan ta bayyana cewa ita ce ta dauki nauyin wannan hari.

Wannan dai ya kasance hari na uku cikin wata guda da ya faru a garin na Karachi.

Wani da ya shaida afkuwar lamarin ya ce abin ya kazanta, in da ya ce an yi ta zazzafar musayar wuta, sai kace a filin yaki.

Ministan harkokin cikin gida a Pakistan Rehman Malik ya yi kira ga al'ummar kasar da su bada tasu gudunmawar wajen yakar kungiyoyin Al- Qaeda da Taliban.

In da ya ce Kungiyar Al- Qaeda da Taliban makiyan Pakistan ne, kuma sun kasance babbar barazana ga Pakistan.

Ya kara da cewa tabbas ba bu wanda zai musanta cewa wannan harin da suka kai ba wai akan Pakistan suka kai shi ba.

Don haka ne ya nemi kowanne dan Pakistan da yayi Allah Wadai da wannan dabi'a, da kuma masu goyawa kungiyoyin Al- Qaeda da Taliban din baya.

Ya sake cewa ba ya jin wadanda suka kai harin sun kasance musulmai balle kuma a ce sun kasance masu son ci gaban Pakistan.

Sai dai sojojin Pakistan din sun bayyana kaddamar da hari domin mayar da martani tare kuma da yi wa mayakan sa kan kawanya.