Gwamnatin Sakkwato da malaman makaranta na takun saka

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A jahar Sakkwato Najeriya an shiga wani takun saka tsakani gwamnatin jahar da kungiyar malamai ta kasa, NUT reshen jahar.

Hakan ya biyobayan wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ne cewar ta bankado wani shirin da kungiyar ta NUT ke yi na zaftare wani kaso daga cikin kudin hutun wannan shekarar da za ta biya malaman jahar a wannan watan.

Kungiyar Malaman ta kira wani taron 'yan jarida na gaggawa inda ta musanta sanarwar da gwamnatin ta fitar a matsayin wani kokarin bata ma ta suna da kuma muzanta ta a idon takwarorinta na sauran jahohi.