Dubunnan jama'a na cigaba da zanga-zanga a Spain

Hakkin mallakar hoto Other

Dubun dubatar jama'a na cigaba da zanga-zanga a tsakiyar Madrid, babban birnin Spain, yayinda suka kalubalanci dokar dake haramta yin zanga-zanga a jajiberin ranar zaben kananan hukumomi.

An fara jerin zanga-zangar ne kwanaki shida da suka wuce da wani zaman dirshan da wasu matasa suka gudanar a babban dandalin birnin na Madrid, don nuna takaicinsu da matsalar rashin aikin yi a kasar inda kashi 45 cikin dari na matasan kasar ke zaman kashe wando.

Masu zanga-zangar dai suna dauke da kellaye inda suka yi rubuce-rubuce, suna masu kiran da aka kawo karshen abun da suka kira rikon kama karya da masu jari hujja ke yiwa kasuwannin kasar.