Matasa na zanga-zanga kan rashin aikin yi a Spain

Hakkin mallakar hoto Reuters

Dubun dubatar matasa a duk fadin Spain na gudanar da zanga-zanga don nuna takaicinsu da matsalar rashin aikin yi da ta yi kamari a kasar da kuma matakan tsuke bakin aljihun gwamnati.

Ana cigaba da zanga-zangar duk da dokar da gwamnati ta kafa ta haramta duk wata zanga-zanga a jajiberin ranar zaben kananan hukumomi.

An fara jerin zanga-zangar ne kwanaki 6 da suka wuce da wani zaman dirshan da wasu matasa suka yi a babban dandalin birnin Madrid, don nuna takaicinsu da tsarin siyasar da ake da shi a kasar. Tun lokacin, matasan sun cigaba da zama a wurin inda suka kafa sansanonin wucin gadi, suna ta nishadi:

Wakilin BBC a Madrid ya ce ga alama zanga-zangar na kara girma, kuma zai yi wuya hukumomin kasar su murkushe masu zanga-zangar saboda tsoron irin munanan abubuwan da za su biyo baya.