Sakataren majalisar dinkin duniya ya iso Najeriya

Ban Ki-moon Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ban Ki-moon

Sakatare-janar na majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon ya fara wata ziyarar aiki ta kwana biyu a Najeriya.

Mr Ban Ki Moon, wanda ya isa Najeriya ne da maraice.

Ya bayyana cewa majalisar dinkin duniyar ta dukufa sosai wajen yaki da mutuwar iyaye mata da yara `yan kasa da shekara biyar da haihuwa, kuma wannan batun na daga cikin dalilin da ya sa ya ziyarci Najeriyar.