Kudancin Sudan ya bayyana kame garin Abyei

Kudancin Sudan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kudancin Sudan

Kudancin Sudan ya bayyana kame garin Abyei na kan iyaka da Arewacin Sudan, wanda kuma ake jayyaya a kansa, a matsayin wani matakin yaki.

Wani kakakin Kudancin Sudan din, Kanar Philip Aguer ya fadawa BBC cewa sojojin Arewacin Sudan sun kai hari a kan yankin, tare da kashe fararen hula da kuma sojojin kudancin Sudan.

Ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki matakin dakatar da abun da ya kira cin zali, yana mai cewa a yanzu, kudancin Sudan ba zai maida martani ba.

A halin da ake ciki kuma, kungiyar agaji ta Medecinsa Sans Frontieres, ta ce mutane dubu 20 sun gudu daga Abyei, wanda duka Arewaci da kudancin Sudan ke ikirarin sun mallaka.

Mau sharhi na fargabar cewa tashin hankalin da ake yi a kan yankin na Abyei zai iya jefa bangarorin biyu cikin wani sabon yankin basasa.