Shugaban Yemen ya ki sa hannu kan yarjejeniyar sauka daga mulki

Hakkin mallakar hoto AP

Shugaba Ali Abdullah Saleh na Yemen ya ki ya sa hannu a wata 'yarjejeniya da za ta share fagen murabis dinsa, ta kuma kawo karshen mummunar zanga-zangar da aka shafe watanni ana yi a kasar.

Gidan talabijin na Yemen din, ya ce zai sa hannu ne kawai a bainar shugabannin adawa, wadanda tuni suka sa hannu a yarjejeniyar a jiya Asabar.

Hakan dai ya haddasa rudani inda har ta kai sai da helikofta aka kwashe jami'an Diflomasiyyar dake shiga tsakani daga Ofishin jakadancin Hadaddiyar Daular Larabarawa dake birnin Sana'a, saboda magoya bayan shugaba Saleh din dauke da makamai sun yiwa Ofishin jakadancin kawanya, suna masu yin watsi da 'yarjejeniyar.