Gudun haihuwar yara mata a Indiya

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Mutane na gudun haihuwar yara mata a Indiya

Kidayar jama'ar da aka yi a kasar Indiya ta yi nuni da cewa, ana samun karancin yara da shekarun su ke kasa da bakwai.

Jami'an dai na ganin cewa akalla an zubar da cikin dake dauke da jarirai mata wajen miliyan takwas a shekaru goma da suka wuce a kasar.

Kulwant tana da yara uku mata masu shekaru 24 da 23 da kuma 20 sai kuma namiji dan shekaru 16.

A shekarun da ke tsakanin haihuwar 'ya'yanta, Kulwanta ta yi ciki sau uku.

A duk lokacin da ta yi ciki, ana tilas ta mata ne ta cire, saboda bayan an dau hoton cikin ana ganin mata ne.

"Uwar mijina ta dade tana yimin gori kan cewa mata kawai nake haihuwa. Ta cewa danta ya sake ni, idan ba zan haifi namiji ba."

Kulwant har yanzu dai bata manta da cikin da ta zubar na farko ba. "Cikin ya kai wata biyar. Kyakyawa ce. Ina kewanta da sauran da na cire cikinsu." In ji Kulwanta bayan ta fashe da kuka.

Kafin ta haifi na miji, Kulwant ta fuskanci matsaloli a rayuwarta musamman irin wulakancin da take sha a wurin surakarta, ta ce akawai lokacin ma da ta so ta kashe kanta.

"Ran surikai na ya baci. Ba sa son mata. Sun fi son maza saboda su rika samun sadaki mai tsoka."

Indiya ta yi dokar hana al'adar mata biyan maza sadaki a shekarar 1961, amma har yanzu al'ummar garin da dama ba su daina al'adar ba.

Mijin Kulwant ya rasu shekaru uku da suka wuce. "Ina ganin Allah ne ya kama mu, bayan da muka kashe 'ya 'yan mu mata ta hanyar zub da ciki. Ina ganin abin da ya sa ya mutu kenan da kuruciyarsa." In ji Kulwant.

Amaren kasashen ketare

Karancin mata a garin Haryana yasa wasu maza a Indiya su fito neman aure a wasu jihohin, amma da yake al'adun sun sha banban, matan na fuskantar kalubale wajen sabo da inda mazajen nasu suke.

Sreeja dai na cikin wadatuwa kuma tana zama da yara biyu da mijin a dakuna biyu dake wani kauye a arewacin jihar.

Image caption Mata na zanga zangar neman hana zubar da cikin yara mata.

"Maza anan kauyen basa barin mata su fita yin aikin. Sun mallake su." In ji Sreeja.

Mijinta, Birbal Singh, nada filin mai yawan aker biyar, kuma direban motar daukar kaya ne.

"Anan babu wani aiki, sai na gona. kuma akwai wahala sosai saboda zafin rana, muna kuma fuskantar rashin ruwan sama anan.

"Mata basu da 'yanci anan, ana yawan cin zarafinsu. A garin mu ana ba mata 'yancin su.

"Anan kauyen idan an gano ka dau ciki kuma mace ce, sai a tilasta miki ki zub da cikin, basa korafin rashin 'yan mata a kauyen, saboda suna ganin idan suna neman aure za su iya zuwa wata jihar.

Taimakon 'ya'ya mata a Bihar

Kusan sama da mata 20 ne suka bayyana a Ofishin gwamnatin na inganta ci gaban yara a kauyen Bihar dake Vidupur.

Yawancin matan dai na tare da 'ya 'yansu mata. Kuma dukkaninsu na dauke da wata takarda fara.

Takardar dai wacce keda mahimmaci na dauke da sunan 'ya mace da ranar haihuwarta da wasu bayanai game da ita.

Takardar wata shaida ce ta ganin an sanya yaran mata cikin wani shirin gwamnati na kare hakkin yara mata.

A karkashin shirin ana sanya kusan dalar Amurka 44 a cikin asusun kowacce yarinya.

Kudin zai rika karuwa ne a yayinda take girma, kuma jami'an sunce kudin zai ninka sau goma kan kudin da aka fara sawa a lokacin da ta kai shekaru 18, kuma ana iya amfani da kudin wajen biyan sadakinta ko kuma biyan kudin makarantar ta.

Wadanda suke fama da talauci ne kawai za su iya amfana da shirin, kuma yara mata biyu ne kawai za'a iya yiwa rajista.

Shirin wanda gwamnatin ta fara a shekarar 2007, an yi shi ne domin mutane su daina zub da cikin yara mata.

"Ana aiwatar da shirin ne domin mutane su rika alfahari da haihuwar yara mata." In ji Irina Sinha wata jami'ar gwamnati.