Aikin Kwamitoci da gwamnati mai karbar gado ta kafa!

A yayin da ya rage kasa da mako guda a mika mulki ga sababbin gwamnatocin da aka zaba, tun yanzu gwamnatoci masu jiran gado suka kafa kwamitoci don tsara yadda za'a karbi mulki.

Kafa irin wadannan kwamitoci dai ba bakon abu ba ne a duk lokacin da aka samu sauyin gwamnati.

Sau da dama dai irin wadannan kwamitoci na da'awar bankado wasu almundahana da gwamnati mai barin gado ta yi, ko da dai ba ko yaushe ne rahoton nasu kan zama dai- dai ba.

A Jihar Kano, tuni Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya kafa irin wannan kwamitin domin bincikar abubuwan da gwamnati mai barin gado ta Malam Ibrahim Shekarau ta yi.

Batun da kwamitin ya gano shine na bacewar wasu kudaden Fensho fiye da Naira biliyan uku.

Sai dai bangaren gwamnati mai barin gadon sun musanta duk wani zargin aikata almundahana.