Kungiyar NATO ta kai samame sansanin soji a Libya

Hakkin mallakar hoto

Dakarun kungiyar kawance ta NATO sun kaddamar da hare- hare ta sama mafi girma a birnin Tripoli tun bayan shigar kungiyar Kasar Libya.

Wannan dai ya kasance wani ci gaba a yakin da take yi da dakarun dake biyayya ga Kanar Gaddafi.

Bama- bamai kimanin ashirin ne ta harba cikin rabin sa'a wanda ya tada hayaki a daukacin birnin.

Kungiyat NATO ta ce ce ta kai hari ne kan wata motar dake dauke da sojojin da za su kai hari kan fararen hula.

Kakakin gwamnatin Libya Mussa Ibrahim ya ce Kungiyar NATO ta jefa bama- baman ne a sansanin kula da sojojin Libya, inda ta halaka kimanin mutane uku tare da jikkata akalla dari da hamsin.