Shugaba Obama ya isa kasar Ireland

Barack Obama da matarsa Michelle Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Obama zai shafe mako guda yana ziyara a Turai

Shugaba Barack Obama na Amurka ya isa kasar jamhuriyar Ireland a matakin farko na ziyarar da zai shafe mako guda yana yi a nahiyar Turai.

Har ila yau shugaban zai ziyarci Burtaniya da Faransa da kuma Poland. A Faransa, zai halarci taron kungiyar kasashen G8, masu karfin masana'antu.

Editan BBC na Arewacin Amurka ya ce batun Afghanistan ne zai mamaye abin da shugabannin za su tattauna da kuma al'amuran da ke faruwa a kasashen Larabawa.

Za a tsaurara matakan tsaro bayan harin da Amurka ta kai wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Osama Bin Laden a Pakistan makwanni uku da suka wuce.

Bayan isarsa birnin Dublin, shugaba Obama zai gana da shugabar Ireland Mary McAleese sannan ya gana da Taoiseach Enda Kenny.

Daga bisani shugaban da mai dakinsa za su ziyarci kauyen Moneygall, Co Offaly, inda kakansa na wurin uwa Falmouth Kearney ya zauna.

An dai tsaurara matakan tsaro a ciki da kewayen kauyen.