Ranar tunawa da Afrika

Hakkin mallakar hoto AP

Yau 25 ga watan Mayu ta kasance ranar da ake bikin Afrika, wanda aka fara tun bayan kafa hukumar tarayyar Afrika a shekarar 1963.

A wannan rana ce dai shugabannin kasashen nahiyar Afirka 30 cikin 32 da suka sami 'yan cin kai, suka sanya hannu akan kafa hukumar a birnin Addis Ababa dake kasar Habasha.

A shekarar 1991 ne kuma hukumar tarayyar Afrikan ta kafa kungiyar kasashen Afirka wato AU.

A bangare guda kuma a yau ne aka shiga rana ta biyu a taron da ake tsakanin India da kasashen Afrika da ake yi a birnin Adis Ababa babban birnin kasar ta Habasha.

Bangarorin biyu na tattaunawa akan batutuwa da suka shafi nahiyar Afrika da kuma wanda suka shafi duniya baki daya.

Batutuwan sun hada da cinikayya, da barazanar satar fasaha, da ta'addanci, da kuma batun sauyin yanayi.