Aman dutse: An soke tashin jirage fiye da 200

Tokar aman dutse Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Aman dutsen ya kawo matsaloli wajen tashin jiragen sama a Turai

An soke tashin jiragen sama fiye da 200 galibi a yankin Scotland da yankin Ireland ta Arewa yayin da giza - gizan tokar aman dutse ya bazu daga Iceland.

Sai dai wani kamfanin sufurin jiragen sama mai rangwame na Ireland, Ryanair, ya soki sokewar.

Bayan da ya tayar da daya daga cikin jiragensa a sararin samaniyar yankin Scotland, Kamfanin na Ryanair ya ce babu wata shedar toka a can.

Sai dai Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Burtaniya ta musanta hakan.

Shugaban Kamfanin Michael O'Leary ya ce Ofishin kula da yanayi na Burtaniya ba shi da cancantar shiga cikin yanke hukunci game da gajimaran tokar:

"Koda a yau filayen jiragen saman Iceland a bude suke, to amma sun rufe filayen jiragen saman Scotland".

Kamfanin sufurin jiragen saman na Ryanair ya ce zai ci gaba da gudanar da zirga-zirgarsa daga Edinburgh a yau.