Ba sai lallai daga Turai za'a nada Shugaban IMF ba

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Direktoci biyar daga Asusun bada lamuni na duniya IMF sun ce ya kamata asusun ya sauya hanyar da yake bi wajen nada Shugaba, kuma ba lallai bane Shugaban ya kasance daga Turai.

Bisa al'ada Shugaban Asusun bada lamuni na duniyar IMF kan kasance ne daga nahiyar Turai.

Amma tun bayan murabus din Dominique Strauss Kahn, Kasashen duniya su ka fara kira kan cewa ba lallai bane Shugaban asusun ya kasance daga Turai, ya kamata ya kasance daga cikin sabbin kasashen da ke tasowa ta fuskar tattalin arziki.

A yanzu haka dai direktoci biyar daga Asusun da ke wakiltar kasashen Brazil da Russia da India da Sin da kuma Afirka ta kudu sun fitar da wata sanarwa akan haka.

Sun ce basu ga alfanun tsohuwar al'adar cewa sai Shugaban ya kasance daga Turai ba, don haka suna kira kan soke wannan al'ada.

Wannan sanarwa dai ta kasance babban kalubale ga nahiyar Turai.

A yanzu haka kasashen Turai da dama sun amince da zabar Ministar kudin Faransa Christine Legard a matsayin wadda ta cancanci hawa kujerar.

Sai dai kuma idan har kasashen biyar da ke kira kan sauya tsarin suka dage kan zabar Shugaba daga kasashe masu tasowa, to wannan zai kasance wani lamari mai wuya da tsauri da kuma sarkakiya da mambobin Asusun 24 za su iya warwarewa.