Fashewa a matatar man Iran

Ahmadinejad na ziyara a matatar Abadan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masana sun yi tsokaci kan matatar ta Abadan

Akalla mutum guda ne ya mutu, yayin da wasu 20 suka jikkata lokacin da wani abu ya fashe a matatar mai ta Iran, lokacin da shugaba Ahmadinejad ke ziyara a matatar.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Fars, ya ce matsalar na'ura ce ta haifar da fashewar.

Jami'ai sun ce hayaki ya turnuke matatar, amma an shawo kan wutar da ta tashi.

Shugaba Mahmoud Ahmadinejad bai samu wani rauni ba, kuma ya yi jawabi a talabijin domin bikin bude matatar man da ke garin Abadan na Kudu maso Yammacin kasar.

Wani babban jami'in Iran ya ce hadarin ba "zagon kasan kasashen duniya ba ne".

"Masana sun yi gargadin cewa bai kamata a kaddamar da matatar man yanzu ba". A cewar Hamid-Reza Katouzian, shugaban kwamitin Makamashi na Majalisar Dokokin Iran.

Wasu rahotannin sun ce mutane biyu ne suka hallaka a lamarin.