Netanyahu ya bayyana manufa a kan Falasdinawa

Benjamin Netanyahu Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ba zai yarda a koma iyayoyin 1967ba

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce a shirye yake ya yi sausauci mai yawa domin cimma zaman lafiya tare da Falasdinawa.

Sai dai ya shedawa wani zaman hadin guiwa na majalisaun dokokin Amurka a Washington cewa wata kasar Falasdinu ta gaba ba za ta kasance da kanun iyakokin da take da su ba kafin yakin Gabas ta Tsakiya na shekarar 1967.

Ya ce, “Mun amince cewar dole wata kasar Palasdinu ta kasance mai girman da zai sa ta kasance mai inganci da yanci da kuma albarka.”

A lokacin jawabi, wanda yana yi ana ta yi masa tabi, Mr Netanyahu ya ce kamata ya yi Shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas, ya yi watsi da yarjejeniyar sasantawarsa da kungiyar Hamas.

Wani kakakin Shugaba Abbas ya ce, jawabin Mr Netanyahu ya kara wani sabon shinge ne kawai ga zaman lafiyar.