Kalubalen Shugabannin Najeriya: Harkar tsaro!

Yayin da ya rage 'yan kwanaki a gudunar da bukukuwan rantsar da Shugaban Kasa da gwamnoni a Najeriya, wani batu da ya zama kalubale ga Mahukuntan Kasar shine na samar da tsaro musamman ma a Jihohin da aka fi samun tashe tashen hankula.

Tun gabanin babban zaben ne dai aka rika samun hare- haren bama- bamai a wuraren tarrukan yakin neman zabe har ya zuwa lokacin zaben a wasu Jihohin.

Jihar Borno dai yanzu haka ita ce ke kan gaba wajen fuskantar wannan kalubale wanda 'ya' yan Kungiyar nan ta Boko Haram ke ikirarin kaiwa hari.

Matsalar tashe tashen hankulan addini da na siyasa ba sabon abu bane a Jihar, lamarin da ya salwantar da rayukan mutane da dama.