Shugaba Obama na ziyara a Birtaniya

Obama Hakkin mallakar hoto bb
Image caption Obama zai gana da Fira Minista Cameron

Shugaba Obama ya gana da Sarauniya Elizabeth a fadar Buckingham, a ziyarar aikin da yake a Birtaniya.

An harba bindiga sama sau arba'in da daya, domin girmama shi, kana kuma shugaban kasar ya duba wani parati da dakaru suka shirya masa.

Yau da maraice kuma Mr Obama da mai dakinsa Michel zasu halarci wata liyafar cin abinci, kafin su kwana a fadar sarauniyar.

Shugaban Amurkar ya gana da praministan Birtaniya, David Cameron.

A gobe aka shirya zasu kara ganawa da Mr Cameron inda zasu tattauna kan batun Afghanistan, da Libya da kuma tattalin arziki na duniya.