Shugaba Sarkozy ya nemi a kawo sauyi a duniyar intanet

Shugaba Sarkozy
Image caption Manyan masu fada aji a harkar intanet na halartar taro a Paris

Shugaban Faransa Nicholas Sarkozy ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnatoci su shifida dokoki da kuma aiwatar da su a kan yadda al'amura suke gudana a duniyar intanet.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wajen wani taro na manyan masu fada a ji a harkokin intanet na duniya wanda yake gudana a kasar ta Faransa ciki har da shugabannin shafukan nan na Google, da Facebook da kuma Microsoft.

Shugaba Sarkozy ya ce dole ne hukumomi su dauki matakan gindaya ka'idoji a harkokin hada-hadar intanet saboda a yanzu intanet ta zama wani bangare na rayuwar mafi yawancin al'ummar duniya.

Har wa yau shugaba Sarkozy ya sanya batun na intanet a cikin jerin abubuwan da za a tattauna a taron kasashen da suka fi ci gaban masana'antu na duniya wato G8 wanda za a gudanar nan gaba cikin makon nan a kasar sa.

Masana da dama na ganin intanet na cimma muhimmin mataki a harkokin kasuwanci da ma rayuwar jama'a a duniya ba ki daya.

Kamfanonin intanet na daga cikin manyan kamfanoni a fagen kasuwanci a sassan duniya daban-daban.

Sai dai wasu shugabannin kamarsu Nicolas Sarkozy na Faransa, suna nuna damuwa kan yadda Amurka ta mamaye fagen na intanet, kuma ana saran zai nemi Amurka ta rage kaka-gidan da ta yi a fagen na intanet.