Christine Lagarde na neman shugabancin IMF

Christine Lagarde Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Christine Lagarde na da goyon bayan kasashen Turai

Bayan shafe kwanaki ana rade-radi, ministar kudi ta Faransa Christine Lagarde, ta bayyana aniyarta ta yin takarar shugabancin Hukumar Lamuni ta Duniya IMF.

Bisa al'ada Shugaban Asusun bada lamuni na duniyar IMF kan kasance ne daga nahiyar Turai. amma a jiya wakilan kasashe masu tasowa, sun nemi a yi watsi da wancan tsari.

Ta shaida wa taron manema labarai a Paris cewa, Shugaban hukumar na baya-bayan nan Dominique Strauss-Kahn, ya yi murabis ne bayanda aka zarge shi da laifin assha da wata ma'aikaciyar otel a Amurka.

Akwai alamun da ke nuna cewa wasu kasashen Turai da dama sun bayyana goyon bayansu ga takararta ta.

Ba sai lallai daga Turai ba....

Daraktoci biyar daga Asusun na IMF sun ce ya kamata asusun ya sauya hanyar da yake bi wajen nada Shugaba, kuma ba lallai bane Shugaban ya kasance daga Turai.

Amma tun bayan murabus din Dominique Strauss Kahn, aka fara kira kan cewa ba lallai bane Shugaban asusun ya kasance daga Turai, ya kamata ya kasance daga cikin sabbin kasashen da ke tasowa ta fuskar tattalin arziki.

A yanzu haka dai daraktoci biyar daga Asusun da ke wakiltar kasashen Brazil da Russia da India da Sin da kuma Afirka ta kudu sun fitar da wata sanarwa akan haka.

Sun ce basu ga alfanun tsohuwar al'adar cewa sai Shugaban ya kasance daga Turai ba, don haka suna kira kan soke wannan al'ada.

Wannan sanarwa dai ta kasance babban kalubale ga nahiyar Turai.

Sai dai kuma idan har kasashen biyar da ke kira kan sauya tsarin suka dage kan zabar Shugaba daga kasashe masu tasowa, to wannan zai kasance wani lamari mai wuya da tsauri da kuma sarkakiya da mambobin Asusun 24 za su iya warwarewa.

Rashin adalci da son kai

Wasu masu sharhi kan harkokin siyasa a Najeriya sun bayyana cewar rashin adalci da son kai na daga cikin dalilan da ya sa kasashen Turai suke dagewa akan sai lallai dan nahiyar ne zai shugabanci Asusun na IMF.

Dr Jibril Abubakar na Cibiyar Raya Demokuradiyya ya shaida wa BBC cewa: "tunda Turawa suna da na su bankin na lamuni, kamata ya yi a ce sun bar sauran kasashe su taka ta su rawar a IMF".

"Suna kokari ne domin su sauya manufar kafa Asusun".

A cewar Dr Jibrin, wannan ya nuna cewa har yanzu Turawa ne ke mulkar kasashen Afrika, kuma wajibi ne kasashen su tashi tsaye domin kwato 'yancinsu.