Obama ya yi jawabi a majalisar Birtaniya

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaba Barack Obama da ke ziyara a Birtaniya, ya bayyana wasu manufofin harkokin waje na Amurka, a wani jawabi ga daruruwan 'yan majalisun dokokin kasar biyu, da kuma sauran manyan bakin da aka gayyata.

A jawabin, cikin majalisar Westminster, mai shekaru dubu da ginawa, Shugaba Obama ya ce wajibi ne Amurka ta kawar da kungiyoyin 'yan ta'adda, da hana yaduwar makaman nukiliya, da kuma tunkarar matsalar sauyin yanayi, kana kuma da yakar yunwa da yaduwar cutuka.

Ya kara da cewa Amurka da Turai su ne zasu ci gaba da kasancewa cibiyoyin daukar duk wani muhimmin mataki a duniya.