"Dole ne Gaddafi ya bar mulki" Obama da Cameron

Shugaba Obama da Cameron Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Obama da Cameron jim kadan bayan sun gama jawabi

Shugaban Amurka Barack Obama da Fira Ministan Burtaniya David Cameron, sun ce wajibi ne Kanal Gaddafi ya sauka daga kan karagar mulkin kasar Libya.

Shugaba Obama ya kuma bayyana cewa yana da muhimmanci ga Burtaniya da Amruka su tabbatar da cewa Afghanistan bata zama wata cibiya da za a rinka kaddamar da hare-hare ba.

Mr Obama ya ce ko kadan ba za'a sasauta matsin lambar da ake yi wa kanar Gaddafi ba.

"Mun ceto rayukan mutane sakamakon matakin da muka dauka. Kuma mun yi haka ne da amincewar Majalisar Dinkin Duniya, kuma da kawancen kasashen duniya da ya hada da na Larabawa".

"Na yi marhaban da hadin kan dake tsakanin Pakistan da Afghanistan".

Tsokaci kan yankin Abiyei

Shugabannin biyu na magana ne bayan kammala tattaunawa a birnin London, inda shugaba Obama ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu.

Sai dai Mr Obama ya nuna damuwa akan abun da ya faruwa a kudancin Sudan dangane da takaddamar da ake akan yankin Abiyei.

Ya ce yayin da ake cigaba da zaman zulumi a yankin Abyei dake kawo barazana ga yajejeniyar zaman lafiya ta sudan, muna aiki tare wurin karfafawa bangarorin gwiwa akan bukatar ganin sun sake nuna aniyar tabbatar da dorewar yarjejeniyar zaman lafiya.