Taron G8 zai maida hankali akan boren kasashen larabawa

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugabanin kasashen duniya sun hallara a garin shakatawa na Deauville da ke Faransa domin hallartar taron kolin kungiyar G8.

Da yake ganawa da manema labarai, kafin a bude taron, Shugaban kungiyar Tarayyar Turai, Herman Van Rompuy ya ce manyan abubuwan da za'a tattauna a taron sun hada tattalin arzikin duniya da kuma boren kasashen larabawa.

Ya ce kungiyar G8 za ta taimaka wajen inganta harkar demokradiyya da kuma bunkasa tattalin arziki ga kusan mutane miliyan dari hudu dake zama a wadannan yankunan.

Taron dai zai samu halartar kasashe Amurka da Kanada da Japan da Rasha da kuma wasu manyan kasashen Turai.

Shugaban Amurka Barack Obama zai halarci taron ne bayan ya kammala ziyarar aiki da ya kai kasar Burtaniya.