Shugaba Goodluck ya fasa halartar taron G8

Shugabannin Faransa da Rasha, Medvedev da Sarkozy Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugabannin Faransa da Rasha, Medvedev da Sarkozy a taron kolin kungiyar G8 A fARANSA

Shugabannin kasashe masu karfin tattalin arzikin masana'antu suna ci gaba da tattaunawa a kasar Faransa.

Shugabannin dai sun bayyana cewa babban abin da za su fi mayar da hankali a kai shi ne halin da tattalin arzikin duniya ya ke ciki, da kuma guguwar sauyin da take kadawa a gabas ta tsakiya.

A halin da ake ciki dai Shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya soke tafiyarsa zuwa taron koli na G8.

A wata sanarwa da mai baiwa shugaban shawara a harkar yada labarai ya sanyawa hannu, Mista Ima Niboro, ta ce soke ziyarar ta biyo bayan tokar aman dutse a kasar Iceland wanda kuma ke kawo cikas ga harkokin zirga-zirga a Turai.

Mahukunta a harkar sufuri sun nuna fargabar cewa za'a iya samun tokar aman dutsen, wanda kuma zai iya kawo cikas ga dawowar Shugaba Jonathan kan lokaci domin a rantsar da shi a kan kujerar shugabanci a ranar Lahadi, bayan zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Afrilu.

An dai sa ran cewa Shugaban kasar zai halarci taron koli na G-8 ne a Deauville da ke Faransa a ranar juma'a, sannan kuma ya dawo ranar Asabar, kafin a rantsar da shi a ranar Lahadi.