Za a bincika rikicin Kaduna

'Yan gudun hijira
Image caption 'Yan gudun hijira a Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa wani kwamiti na mutum 11 don gudanar da bincike akan rikicin da yayi sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyi a Jihar.

Ana sa ran kwamitin zai gabatar da shawarwari a bisa yadda za a guji afkuwar wani abu makamancin haka a nan gaba.

Rikici ya barke ne a jihar ta Kaduna bayan zaben shugaban kasa na watan Aprilu.

Kungiyar Human Rights Watch wadda ke kare hakkin bil dama tace sama da mutane 800 ne suka halaka, da dama kuma suka samu raunika a sanadiyar rikicin.

Haka nan kuma akwai mutane sama da dubu hudu da a yanzu haka suke zaune a sansanonin yan gudun hijira dake watse a jahar ta kaduna, sanadiyyar rasa gidajensu.