Za a kafa hukumar da za ta binciko mai a arewacin Najeriya

Majalisar wakilan Najeriya ta amince da kudurin dokar da zai bayar da damar kafa wata hukuma da za ta binciko mai a yankin arewacin kasar.

Majalisar ta ce kafa hukumar, wadda za ta kasance mai cin gashin kanta, zai bayar da damar matsa kaimi wajen bincikowa, da kuma hako mai a arewacin kasar.

A baya dai an sha gudanar da bincike kan yiwuwar hakar mai a yankin, sai dai yunkurin ya yi ta cin karo da cikas.