An kama wani wanda ake zargi da kisan kare dangi a Rwanda

Kotun Majalisar Dinkin Duniya dake shari'ar laifukkan yaki a Rwanda ta ce an kama wani jagora cikin mutanen da ake zargi da aikata kisan kare dangi.

An kama Bernard Munyagishari ne a jamhuriyar Dimokradiyar Congo, bayan ya shafe shekaru sha bakwai yana buya.

Ana zarginsa ne da shirya kisan yan kabilar Tutsi da wasu yan Hutu masu sassaucin ra'ayi a lardin Gisenyi dake yammacin kasar.

Zai fuskanci tuhumar kisan kare dangi, da kisan kai, da kuma aikata fyade.

Har yanzu akwai wasu 'yan kasar ta Rwanda su tara da ba aji duriyarsu ba, da su ma ake zarginsu da kasancewa a sahun gaba wajen shirya kisan kiyashin da aka aikata a 1994--inda aka kashe dubban daruruwan mutane.