Shugaban Abkhazia ya mutu a birnin Moscow

Sergey Bagapsh
Image caption Marigayi Sergey Bagapsh, Shugaban Abkhazia

Rahotannin da ke fitowa daga birnin Moscow na cewa shugaban kasar Abkhazia wadda ta balle daga Georgia, Sergey Bagapsh, ya mutu a wani asibiti yana dan shekaru sittin da biyu.

Kamfanin dillancin labarai na Interfax ya ce shugaban na Abkhazia ya mutu ne bayan an yi masa wani aikin fida mai sarkakiya da ya shafi huhu a babban birnin na Rasha mako guda da ya gabata.

Yankin Abkhazia dai ya balle ne daga Georgia a shekarar 1992, amma Rasha da wadansu kasashe kalilan ne kawai suka amince da shi a matsayin kasa ’yantacciya.

Tuni dai aka ayyana mataimakin shugaban kasar, Alexander Ankvab, a matsayin shugaban kasa na riko.