An bindige wani mai fafutuka a Brazil

Masu zanga-zangar adawa da sare itatuwa a Brazil Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga-zangar adawa da sare itatuwa a Brazil

An bindige wani mai fafutukar kare muhalli har lahira a Brazil.

Wannan kisa dai shi ne na uku da aka yiwa masu fafutukar kare muhallin a cikin makon nan.

Wadansu ne dai a kan babur dauke da bindiga suka harbe marigayin mai suna Adelino Ramos a Jihar Rondonia da ke yankin nan mai albarkatun gandun daji na Amazon.

Kwanaki uku da suka gabata ma dai an kashe wadansu masu fafutukar kare muhallin su biyu a yankin na Amazon wanda ke arewacin kasar ta Brazil.

Dukkan wadanda aka kashe din dai suna matukar adawa ne da sare bishiyar katako ba bisa ka'ida ba, kuma dama anyi ta yi musu barazana.