Ba zan je rantsar da Jonathan ba -Buhari

Janar Muhammadu Buhari mai ritaya
Image caption Janar Muhammadu Buhari mai ritaya

A Najeriya, dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar CPC a zaben da ya gabata, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ya ce ba zai halarci bikin rantsar da Shugaba Goodluck Jonathan ba ranar Lahadi.

A cewar Janar Buharin, a farkon makon da muke ciki ne dai gwamnatin—ta hannun ofishin da ke kula da harkokin tsofaffin shugabannin kasa a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya—ta gayyace shi wajen bikin rantsar da Dakta Jonathan a matsayin sabon shugaban kasar.

“An aiko min da katin [gayyata]…akwai kuma [lambar] waya ta ba da amsa; to na ce a ba da amsa cewa ba zan samu damar zuwa ba”, in ji Janar Buhari.

A hirarsa da wakilin BBC a Kaduna, Janar Buhari ya kuma kalubalanci wadanda suka sanya ido a zaben da ya gabata cewa su fito da shaidun da ke nuna cewa an gudanar da sahihin zabe a yankunan Kudu Maso Kudu, da Kudu Maso Gabashin kasar:

“Wadanda suka je suka sa ido a kan zaben Kudu Maso Kudu da Kudu Maso Gabas da Kudu Maso Yamma su fadi abin da ya auku a can kudu—ko ko sa idon zaben na su a Arewa kawai aka sa su?”

Da ya ke mayar da martani a kan cewa jam’iyyar sa ta CPC ba ta yi aiki a sassan na kudancin Najeriya ba, kuma ba ta da magoya baya da yawa, Janar Buhari cewa ya yi:

“Akwai gaskiya cikin wannan magana; muna da magoya baya a Arewa fiye da Kudu—amma a Kudun ma muna da mutanen mu.

“Tunda wannan magana tana gaban shari’a, kuma mutanen mu na Kudu din wadanda aka kora, aka hana su su yi zabe; ko wadanda aka kashe su, ai an rubuta takardu wadanda za mu kai gaban shari’a saboda haka ba zan yi magana a kan wannan ba”.