Bin Hammam ya fasa takarar shugabancin FIFA

Dan takarar shugabancin FIFA, Muhammad bin Hammam Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan takarar shugabancin FIFA, Muhammad bin Hammam

Daya daga cikin mutane biyun da ke neman a zabe su a matsayin shugaban Hukumar Kula da Wasan Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ranar Laraba ya janye daga takarar.

Dan kasar Qatar Muhammad Bin Hammam ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na intanet, wadda a ciki ya ke cewa ya fasa takara da shugaban hukumar ta FIFA mai ci, Sepp Blatter.

Bin Hammam ya ce ya janye daga takarar ne saboda wadansu abubuwa da suka faru a baya-bayan nan wadanda suka shafi aikinsa da mutuncinsa.

Yau ne dai ake sa ran daga shi Bin Hammam din har Sepp Blatter za su gurfana a gaban kwamitin da'a na hukumar ta FIFA.

An kira zaman kwamitin ne bayan wani jami'in hukumar ta FIFA ya zargi Bin Hammam da cin hanci da rashawa; zargin da ya musanta.

Janyewar ta sa dai na nufin yanzu dan takara daya tilo ne ya rage, wato Sepp Blatter, wanda ya kwashe shekaru goma sha ukun da suka wuce yana shugabancin hukumar.