Ana kaddamar da sabon shugaban Najeriya

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

A Najeriya, a yanzu haka an fara bikin rantsar da shugaban kasar, Dakta Goodluck Jonathan, da mataimakinsa, Architect Namadi Sambo, da wadansu gwamnoni, bayan nasarar da suka samu a zaben da aka yi a kasar a watan Afrilun da ya gabata.

Gwamnatin Najeriyar ta shirya gagarumin biki saboda wannan rana, kuma shugabannin wasu kasashe arba’in daga nahiyar Afrika da sauran bangarorin duniya, da kuma jakadu sun halarra.

An dai kwashe kusan mako guda ana wadansu hidimomi a matsayin sharar-fage ga wannan ranar, wadanda suka hada da tarurruka da sabon shugaban kasar ya yi da ’yan kasuwa da matasa da kuma addu’o’i a wuraren ibada.

A bikin na yau an tsara jami’an tsaro da dangoginsu da kuma ’yan makaranta sun yi maci, baya ga wadansu wasananni na nishadantarwa gami da liyafar da aka shirya don debe kewa ga mahalarta.

Dangane da tsaro kuwa tun ranar Alhamis din da ta gabata aka fara datse wadansu hanyoyin da kan dangana da dandalin Eagle Square, inda za a yi bikin rantsarwar, yayin da jami’an tsaro daban-daban ke ci gaba da yin sintiri a ciki da kewayen dandalin.

Wannan biki dai, kamar yadda rahotanni suka nuna, zai cinye kusan naira miliyan dubu biyar, al’amarin da ya sa masu rajin kare dimokuradiyya irin su Awwal Musa Rafsanjani ke sukar bikin saboda, a ra'ayinsa, ko don mace-macen da aka yi lokacin zabe bai dace a yi bikin ba.

“Gaskiya wannan kudi da aka ce za a kashe ya yi yawa, ganin yadda Najeriya da ‘yan Najeriya ke fama da talauci....

“Na biyu, an ce an kashe sama da mutum dari takwas bayan wannan zabe; saboda Allah ya za a yi, maimakon ka yi nadama ka zo kana kashe wadannan kudade?”

Amma Sakataren Gwamnatin Najeriya, Alhaji Mahmud Yayale Ahmad, ya ce kambama kudin bikin kawai ake yi:

“Gaskiyar abin shi ne abin da za mu kashe, kwata-kwata, biliyan daya ne; kuma biliyan dayan ma har yanzu ba mu kai ga kasheta ba.

“Amma muna fata, in an kare, [in ya haura biliyan dayan] abin da zai haura bai taka kara ya karya ba”.

Game da yadda wasu ke ganin cewa ya kamata a fasa bikin don rashin da aka yi kuwa, Ministan Yada Labaran kasar, Mista Labaran Maku cewa ya yi:

“Ko ana yaki ne, in lokacin canji ya zo dole ne a godewa Allah; Allah Ya kawo sabon shugaba”.

Duk da irin hanzarin da mahukuntan Najeriya ke kawowa, wadansu ’yan kasar na da ra’ayin cewa babu dalilin kashe ko da naira miliyan dubu ne a kan bikin rana daya, na karbar ragamar mulki.