Yunkurin sasanta Sojoji da 'yansanda a Najeriya

Image caption Jami'an tsaro a Najeriya na aiki tare

A Najeriya rundunar yan sandan kasar da kuma ta sojoji sun yi taro na musamman domin duba musabbabin hatsaniyar da ta faru tsakanin wasu jami'an 'yansandan da kuma na sojoji ranar Lahadin da ta gabata a jihar Legas, inda duka bangarorin biyu suka yi a sarar jami'ansu.

A taron manema labaran da suka gabatar bayan kammala tattaunawar, Sufeto janar na yansanda Hafizu Ringim da kuma Babban hafsan sojojin kasa Laftanal Janar Azubuike Ihejirika, sun yi alkawarin kafa kwamitin hadin gwiwa da zai gudanar da bincike kan musababbin lamarin, tare da nemo hanyoyin da za a kaucewa sake faruwar hakan.

A cewar babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Lieutenant General Azubuike Ihejirika, ya zo hedkwatar rundunar 'yansandan ne domin taya su jimamin rasa jami'ansu da suka yi a hatsaniyar da ta faru a jihar ta Legas, domin a cewarsa abu ne na bakin ciki ga duka bangarorin biyu.

Ya kuma ce rundunar sojin ana ta bangaren za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin makamancin wannan lamari bai sake faruwa ba.

Dangantaka

Shi kuwa Sufeto janar na yansandan Najeriyar Hafizu Ringim, cewa yayi lamarin ya bude sabon shafi a tarin dangantaka tsakanin bangarorin tsaron kasar, domin wannan ne karo na farko da suka zama a irin wannan mataki domin shawo kan makamantan wannan matsala.

Bangarorin biyu sun kuma sha alwashin kafa kwamiti na hadin gwiwa domin gudanar da bincike kan lamarin da kuma nemo hanyoyin da za a magance shi kwata-kwata.

Sai dai sun ki bada karin haske kan yadda kwamitin zai gudanar da ayyukansa da kuma tsawon lokacin da za a shafe ana gudanar da binciken, suna masu cewa za su dinga yiwa yan jarida bayani lokaci zuwa lokaci.

A baya ansha samun fadace-fadace tsakanin 'yansanda da kuma sojoji a Najeriya, wadanda maimakon aikinsu na hana jama'ar gari yin fadan, su ke bigewa da yi a tsakaninsu.

Abinda ya sa masu sharhi ke ganin ba alheri bane ga rundunonin tsaron kasar.

Lamarin na ranar lahadin dai, ya janyo asarar rayuka ga bangarorin biyu, sai dai sun ki tabbatar da cikakken adadin rayukan da aka yi asara, suna masu cewa bincike ne kawai zai tabbatar da hakan.