Shugaba Obama na kammala ziyara a Poland

Shugaba Obama na Amurka Hakkin mallakar hoto APTN
Image caption Shugaba Obama na Amurka

A yau Shugaba Obama na Amurka ke kammala ziyarar da ya kai kasashen Turai a birnin Warsaw, inda zai gana da shugabannin kasar Poland.

Shugabannin na fatan Mista Obama zai yiwa kasar sakayya dangane da soke shirin Shugaba Bush na girka makaman kariya daga harin makami mai linzami.

Shugabannin Poland dai ba su ji dadi ba da Shugaba Obama ya dakatar da shirin na samar da garkuwa daga harin makami mai linzami a kasar ta Poland.

A tunaninsu wannan bayar da kai ne ga kasar Rasha, kuma alama ce ta rashin nuna damuwa da kasar Poland.

Zai yi wuya matsayin Mista Obama a kan batun ya sauya; to amma shugabannin na Poland na neman tallafi ta fuskar tattalin arziki a dangantakarsu da Rasha.

Kasar ta Poland dai tana da dimbin albarkatun gas a karkashin kasa wadanda kasashen Jamus da Rasha ba sa so a hako.

Jamus na adawa da hako gas din Poland din ne saboda dalilai na kare muhalli yayin da Rasha kuma ba ta so ne watakila saboda ita ce ke samar da akasarin gas din da ake amfani da shi a daukacin yankin.

Fatan shugabannin na Poland dai shi ne Shugaba Obama ya goyi bayan bude ma'adinan na gas da taimakon kamfanonin samar da makamashi na Amurka.