An hallak kwamandan 'yan sanda a Afghanistan

Daoud Daoud, babban kwamandan 'yan sandan Afghanistan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Daoud Daoud, babban kwamandan 'yan sandan Afghanistan

An hallaka babban kwamandan rundunar 'yan sanda na yankin arewacin Afghanistan, a wani hari na kunar bakin wake.

Janar Daoud Daoud ya hallaka ne tare da shugaban rundunar 'yan sandan Lardin Takhar, lokacin da dan kunar bakin-waken, sanye da kayan 'yan sanda, ya tarwatsa kansa, yayin da mutanen ke barin wani zauren taro, a gidan gwamnan jahar.

Wasu sojoji biyu 'yan kasar Jamus ma sun rasa ransu, tare da wasu masu tsaron lafiya su biyu. Mayakan Taliban sun ce sune suka kai harin.

Wakilin BBC ya ce, kisan Janar Daoud Daoud, wata nasara ce da 'yan Taliban za su yi ta farfaganda akai, kuma koma-baya ne ga kamfen din hare-haren da ake kaiwa 'yan gwagwarmaya a arewacin AFghanistan.