An rantsar da Shugaba Goodluck Jonathan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

An rantsar da shugaba Goodluck Jonathan da kuma mataimakinsa Namadi Sambo a wani kaisaitaccen biki a Abuja.

An dai rantsar da shugaban kasar ne da wasu gwamnonin kasar sakamakon nasasar da su ka samu a zaben watan Afrilu

Gwamnatin Najeriyar ta shirya gagarumin biki a wurin rantsarwar, yayinda shugabannin wasu kasashe daga nahiyar Afrika da sauran bangarorin duniya, da kuma jakadu suka hallara.

An dai kwashe kusan mako guda ana wadansu hidimomi a matsayin sharar-fage ga wannan ranar, wadanda suka hada da tarurruka da sabon shugaban kasar ya yi da 'yan kasuwa da matasa da kuma addu'o'i a wuraren ibada.

Alkawura

A jawabin da yayi bayan rantsarwar, Shugaba Goodluck Jonathan ya jinjinawa 'yan Najeriya, saboda irin hakurin da suka nuna wajen tabbatar da cewa demukradiyya ta kafu a kasar, ta hanyar tabbatar da sun zabi shugabannin da suke da kwarin gwiwa akansu.

Shugaba Jonathan dai ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba, wajen ganin ya shimfida sauye sauyen da zasu inganta rayuwar al'ummar kasar.

Ya ce gwamnatinsa za ta maida hankali ne, wajen inganta kanana masana'antu domin farfado da tattalin arzikin kasar.

Har wa yau shugaban kasar ya bayyana cewa za'a ci gaba da mai da hankali wajen samarda hasken wutan latarki da harkar kiwon lafiya da kuma inganta harkar noma, domin samarda aikin yi ga dubban matasa a kasar.

Shugaba Jonathan dai ya nemi goyon bayan al'ummar kasar wajen ganin gwamnati ta cika alkawuran da ta dauka na inganta rayuwarsu.

Tsaro

Dangane da tsaro kuwa tun ranar Alhamis din da ta gabata aka fara datse wadansu hanyoyin da kan dangana da dandalin Eagle Square, inda za a yi bikin rantsuwar, yayin da jami'an tsaro daban-daban ke ci gaba da yin sintiri a ciki da kuma kewayen dandalin.

Image caption An tsananta jami'an tsaro a babban birnin Tarraya Abuja.

A bikin na yau an tsara jami'an tsaro da dangoginsu da kuma 'yan makaranta sun yi maci, baya ga wadansu wasananni na nishadantarwa gami da liyafar da aka shirya don debe kewa ga mahalarta.

An dai kuma katse duk wata layin wayar salula a cikin birnin Abuja a yayinda ake bikin rantsarwar.

Wannan biki dai, ya lashe kusan naira miliyan dubu biyar, al'amarin da ya sa masu rajin kare dimokuradiyya irin su Awwal Musa Rafsanjani ke sukar bikin saboda, a ra'ayinsa, ko don mace-macen da aka samu lokacin zabe bai dace a yi bikin ba.

"Gaskiya wannan kudi da aka ce za a kashe ya yi yawa, ganin yadda Najeriya da 'yan Najeriya ke fama da talauci....

"Na biyu, an ce an kashe sama da mutum dari takwas bayan wannan zabe; saboda Allah ya za a yi, maimakon ka yi nadama ka zo kana kashe wadannan kudade?"

Bayanai kan Goodluck

An haifi Goodluck Ebele Jonathan a yankin Niger Delta a watan Nuwamba ta shekerar 1957 ga iyalin dake kera kwale-kwale.

Ya yi karantu dabobi kuma ya yi aiki a matsayin me sa ido akan harkar ilimi, malami a jami'a da kuma jami'in kare muhalli kafin ya shiga siyasa a shekerar 1998. Yana kuma da digirin digir-digir a fanin dabobi.

Jonathan ya yi nasara a zaben 1999 a matsayin mataimakin gwamna a jihar Bayelsa, daya daga cikin jihohi shida a yankin Niger Delta mai arzikin mai.

Ya kasance gwamnan jihar a shekerar 2005 bayan da aka tsige ubangidansa daga mukamin gwamnan jihar.

Jam'iyyar PDP ta amince masa ya tsaya a matsayin mataimakin shugaban kasa na marigayi Umaru Musa Yar'adua a zaben shekerar 2007.

An dai ranstar da Mr Jonathan a matsayin shugaban kasar Najeriya a watan Mayu ta shekerar 2010, kwana daya bayan rasuwar Yar'adua.

A ranar goma sha hudu na watan janairu, Mr Jonathan ya yi nasara a matsayin dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasar da aka yi a watan Afrialu, inda ya samu galaba akan dan takarar Arewacin kasar daya tilo da aka amince da shi wato, Alhaji Atiku Abubakar.

Sai dai yakin neman zaben Jonathan ya janyo cece-kuce saboda yarjejeniyar dake tsakanin 'yayan jam'iyyar da ta amince da tsarin karba -karba tsakanin Arewaci da galibin su musulmai ne da kudanci da galibinsu mabiya adinin Krista ne.

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Namadi Sambo

An haifi Muhammad Namadi Sambo a watan Augusta ta shekerar 1954, a jihar Kaduna dake Arewacin Najeriya.

Sambo mutum ne da ya kware a hakar fasahar zane zanen gidaje.

Ya kuma rike mukamai a ma'aikatar ayuka da sufuri da kuma gidaje a shekarun 1980, ya ajiye aiki a shekarun 1990 inda ya koma dan kasuwa amma ya shiga hakar siyasa a matsayin gwamnan jihar Kaduna a shekerar 2007.

Ya taka rawar gani akan harkar tsaro a lokacin da ya ke rike mukamin gwamna, abun da ya kasance wata babbar matsala a jihar biyo bayan shekarun da aka shafe ana samun tashe tashen hankula.