Kungiyar Oxfam ta ce farashin abinci ka iya tashi

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Kungiyar agaji ta Oxfam ta yi gargadin cewa farashin kayan abinci zai iya ninka yanda yake nan da shekaru ashirin masu zuwa, a saboda matsolin da suka danganci dumamar yanayi da kuma rashin zuba jari a bangaren harkar noma.

A wani sabon rahoto da kungiyar ta Oxfam ta fitar ta ce a yayin da ake saka ran adadin jama'a a duk fadin duniya a shekarar 2050 ya kai biliyan tara, abubuwan da ake nomawa sun ragu da kashi biyu tun a shekarar 1990.

Rahoton dai na yin kira ne ga shugabannin kasashen duniya da su zuba jari a wani asusu domin shawo kan sauyin yanayi.

Rahoton ya kuma yi kira kan yin gagarumin sauyi a bangaren harkar noma kayan abinci da kuma samar da wutar lantarki a manya da kananan kamfanonin harkar noma da sarrafa abubuwan da aka noma.