Jamus za ta rufe tashoshin nukiliya

Shugabar Jamus, Angela Merkel Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jamus za ta rufe tashoshin nukiliyarta

Gwamnatin hadin gwiwa ta kasar Jamus ta yanke shawarar rufe dukkan tashoshin nukiliyar kasar nan da shekarar 2022.

A watan Maris din da ya gabata ne dai aka rufe tashoshin nukiliya bakwai wadanda suka fi tsufa a kasar, bayan masifar da ta aukawa tashar nukiliya ta Fukushima da ke Japan.

Yawancin ma'aikatun kasar na amfani da tashoshin nukiliyar ne wajen samun wutar lantarkin da suke amfani da ita.

Sai dai gwamnatin ta ce za ta maida hankali wajen amfani da hasken rana, da sauran hanyoyin samun makamashi wadanda ba za su yi illa ga muhalli ba.