Tashin bama bamai a wasu jihohin Najeriya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A 'yan shekarun nan ne dai Najeriya ta fara fuskantar kalubalen tashin bama bamai

A jihar Bauchi dake arewa maso gabashin Najeriya, akalla mutane goma sha hudu ne suka rasa rayukansu wasu kusan talatin kuma suka jikkata, a sakamakon tashin bama-bamai da ya auku a ranar Lahadi da dare a wata kasuwar barikin soja wato Mami Market. Kawo yanzu ba a tabbatar da ko su wane ne suka kai harin ba amma hukumomi sun ce suna kan bincike.

Wadanda suka shaida abin da ya faru, sun ce sun ji karar fashewar wasu abubuwa guda uku.

Wadanda suka jikkata sakamakon fashewar bom din na can suna karbar magani a wani asibitin jihar.

Bam a Zaria

Jami'an tsaro sun ce bama-bamai biyu sun tashi a garin Zaria dake jihar Kadunan Najeriya inda ya jikkata mutane hudu.

Kakakin hukumar 'yan sandan Jihar, Aminu Lawal ya ce bama-baman sun tashi a lokuta dabam-daban ne a garin, inda na farko ya tashi a daren ranar Lahadi sannan na biyu ya tashi da safiyar Litinin.

"Na farkon dai ya tashi ne a wani gidan giya inda ya raunata mutane biyu, sai kuma na biyu da ya tashi a wata unguwa ya raunata wasu yara biyu." In ji Aminu Lawal.

Kakakin 'yansandan ya ce har yanzu dai ba'a san mutanen da suka kaddamar da harin ba.

Bam a Zuba

Zancen ma haka yake a garin Zuba dake kusa da Abuja, inda bam ya tashi a daren jiyya a wani gidan shan giya.

Shugaban hukumar bada agaji na gaggawa, Alhaji Sani Sidi ya ce mutane biyu sun mutu sanadiyar harin a yayinda wajen guda goma sha daya da suka jikkata suna asibiti.

A Maiduguri babban birnin jihar Borno ma, wani bam ya tashi kusa da wata motar sintiri ta sojoji da safiyar yau.

Mai magana da yawun jami'an tsaron Abubakar Abdullahi ya ce; "Wani bam ya tashi kusa da motar da muke sinitri da safiyar yau dinan da misalin karfe 7.30, amma babu wanda ya ji rauni."