Jonathan ya saka hannu a dokar samun bayanai daga gwamnati

Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Goodluck Jonathan

Kungiyar 'yan jarida ta Najeriya, NUJ ta yi marbahin da matakin da da shugaba Goodluck Jonathan ya dauka na sa hannu a shirin dokar nan ta samun bayanai daga gwamnati, watau Freedom of Information Bill a Turance.

A ranar Asabar din da ta wuce ne dai, Dr Goodluck Jonathan ya sa wa shirin dokar hannu, kwana daya bayan da majalisar dokokin kasar ta tura ma sa shirin dokar.

A karkashin dokar dai, ya zama wajibi ne ga gwamnati ta mika duk wasu bayanai da 'yan jarida ko jama'a ke bukata a cikin mako daya, kuma laifi ne wani jami'in gwamnati ya lalata bayanan da ke ajiye a ofishinsa.