Jonathan ya rantsar da Anyim da Azazi

Hakkin mallakar hoto AP

A Najeriya, shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan ya fara nadin jami`an da zai kafa sabuwar gwamnati da su.

Wadanda ya fara nadawar sun hada da tshohon shugaban majalisar dattawan kasar, senata Anyim Pius Anyim, wanda aka rantsar a yau a matsayin sakataren gwamnatin tarayya, yayin da ya sake tabbatar wa janar Andrew Azazi mukaminsa na mai baiwa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro.

Sai dai wasu `yan kasar na ganin sake nadin da aka yi wa Andrew Azazin kamar wata alama ce da ke nuna cewa kusan jami`an tsohuwar gwamnatin da ta gabata ne kawai za a sake kafa sabuwar gwamnatin da su.

Kasashen duniya da masu zuba-jari da dama dai sun zuba wa Najeriyar ido wajen ganin irin mutanen da sabuwar gwamnatin kasar za ta kunsa.