Takaddama tsakanin Afghanistan da Nato

Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Hamid Karzai yana sukar dakarun tsaron Nato

Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai, ya ce kungiyar tsaro ta Nato "ba ta da ikon" kaddamar da hari kan gidajen jama'a a kasar.

Ya ce dakarun Nato na kan hanyar zamowa "'yan mamaya" idan suka ci gaba da kai hare-haren da ke kashe fararen hula.

Kalaman na sa na baya-bayan nan, na zuwa ne bayan da ya yi Allah wadai da harin da Nato ta kai ranar Asabar, wanda ya kashe fararen hula 14 a Kudancin kasar.

Wakilin BBC Paul Wood a birnin Kabul ya ce kalaman na nuna irin barakar da ke tsakanin Mr Karzai da Nato.

Wannan dai dadaddiyar manufa ce ga Mr Karzai, amma babu tabbas kan matakin da zai dauka idan karin fararen hula suka ci gaba da mutuwa a yakin da Nato ke yi da Taliban, a cewar wakilin BBC.

Shugaban ya ce wannan ne kashedi na karshe kan Nato.

"Wajibi ne Nato ta san cewa ba ta da ikon kai irin wadannan hare-hare kan jama'ar Afghanistan, kuma ba za mu kara amincewa da su ba," kamar yadda Mr karzai ya shaidawa taron manema labarai a Kabul.

"Idan ba su daina kai hari kan jama'ar Afghanistan ba, to zamansu a kasar zai kasance na 'yan mamaya kuma ba tare da amincewar jama'ar Afghanistan ba".

Nuna damuwa

Harin na ranar Lahadi wanda aka nufi masu tayar da kayar baya a gundumar Helman, ya samu wasu gidajen farar hula biyu. Jami'ai sun ce duka mutanen da suka mutu mata ne da kananan yara.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dakarun Nato kan kai hare-hare ta sama a lokuta da dama

Kungiyar Nato ta nemi afuwa. Wata sanarwa daga wani babban Janar ta ce manufarsu ita ce ta kare fararen hula, kuma suna daukar hakan da muhimmanci.

A daidai lokacin da ake zargin masu fafutuka wajen haifar da kisan fararen hula, masu aiko da rahotanni na cewa kisan fararen hular na haifar da damuwa a tsakanin jama'ar kasar.

A baya hakan ya haifar da zanga-zangar a kan titunan Afghanistan, inda jama'a ke fitowa domin nuna korafinsu.

A gefe guda dai manyan dakarun Nato na cikin damuwa game da matsayar ta shugaba Karzai.

Sai dai ana ganin akwai yiwuwar ci gaba da kai irin wadannan hare-haren.