Za'a tisa keyar Mladic kotun duniya

Kotun shari'ar laifukkan yaki ta Sabiya, ta yi watsi daukaka karar da tsohon kwamandan Sabiyawan Bosniya, Ratko Mladic ya yi, kan yunkurin mika shi ga kotun shari'ar laifukkan yaki ta duniya dake Hague, inda ake tuhumarsa da kisan kare dangi.

Wakilin BBC ya ce Lauyan Mr Mladic dai ya kawo hanzarin cewa, ba shi da koshin lafiyar da zai iya jure ma zuwa Hague, gurfana a gaban kotu.

A yanzu abin da ya rage shi ne sai Ministan shari'a na Sabiya ya rattaba hannu a kan takardar mika shin, kafin a sa Mr Mladic cikin jirgin sama zuwa Hague. Akwai rahotanin dake cewa mai yuwa a kai shi can nan gaba a yau Talata da yamma.