Gwamnan babban bankin Afghanistan yayi murabus

Hamid Karzai, Shugaban Afghanistan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hamid Karzai, Shugaban Afghanistan

Gwamnan babban bankin Afghanistan, Abdul Qadeer Fitrat, ya ce yayi murabus.

Da yake magana daga Amirka, mista Fitrat ya gayawa BBC cewa, yana jin rayuwarsa na cikin hadari, yayin da yake kokarin gudanar da bincike akan wani babban abun kunyar da ya shafi cin hanci da rashawa, a bankin Kabul mai zaman kansa.

A bara ne dai Kabul Bank ya durkushe, bayan yayi hasarar da aka kiyasta ta kai ta dala miliyan dari biyar, ta hanyar sata.

Tsoffin masu hannun jari a bankin sun hada da 'yan uwan shugaban kasar, Hamid Karzai, da kuma na kurkusa da shi.

Wata wakiliyar BBC ta ambato gwamnan babban bankin na cewa, manyan jami'ai a Afghanistan na yin zagon kasa ga kokarin da yake na kwato kudaden daga wadanda suka sace su.