Mutane sun hallaka a hare-hare a Maiduguri

Harin 'yan Boko Haram a Najeriya
Image caption Harin 'yan Boko Haram a Najeriya

A Najeriya, wasu da ake zargin 'yan gwagwarmayar Musulunci ne sun kai hari a yau din nan, a birnin Maiduguri.

Rundunar sojan kasar ta ce, mutane ukku sun hallaka, kuma dayawa sun jikkata, a lokacin da wasu bama-bamai suka fashe, a wani ginin jami'an kwastan da ke Maidugurin.

Jiya Lahadi mutane fiye da ashirin ne suka mutu, a wasu hare-hare ukku da aka kai a birnin.

An sami yawancin mace-macen ne a lokacin da wasu mutane akan babura, suka jefa nakiyoyi a cikin wata mashaya da ke cike makil da jama'a.

Jami'an 'yan sanda sun ce yin kungiyar Boko Haram ce, wadda a kwanakin baya ta kai harin bam a hedkwatar 'yan sandan da ke Abuja.

A cikin wata sanarwar da ta bayar, kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International, ta ce ya kamata kungiyar ta Boko Haram ta daina kai hare-hare akan fararen hula.